Wata kafa da ke nuna goyon baya ga kungiyar al-Qaeda ta ba da rahoton cewa ?ungiyoyin ta’adda da ke hamayya da juna sun gwabza fa?a a Najeriya kuma wani ?azamin fa?a ya ?arke tsakanin shugabbanin IS a Somalia.
Kafar Thabat ta wallafa labari a mujallarta ta mako mako a kafar RocketChat da ta saba turo labarai game da rikicin.
Ta ce mayakan IS sun gwabza fa?an ne a ?auyen Sunawa da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.
Kuma rikicin ya ?arke ne bayan maya?an IS sun sace mata da dama da ke da ala?a da Boko Haram inda kuma Boko Haram ta ?addamar da hari kan sansanin IS kuma a cewar kafar ta kashe maya?an IS da dama tare da ku?utar da matan.
A 2015 shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya sanar da goyon bayansa ga IS kafin daga baya ?angaren ?ungiyar ya sauya suna zuwa ISWAP.
Daga baya Shekau da wasu mabiyansa suka ?alle daga IS bayan ta na?a sabon shugaba. Kuma an sha bayar da rahotannin fa?a tsakanin ?ungiyoyin a yankin Tafkin Chadi.
Kafar Thabar kuma ta bayar da rahoton cewa an gwabza ?azamin fada tsakanin maya?an IS a Somalia kan neman shugabanci. Kuma a cewar kafar rikicin ya ?arke ne bayan ?aya daga cikin shugabannin ?ungiyar Abdel Qadir al-Mumin ya kwanta rashin lafiya a watan Disamba.