Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Borno: An Dam?e Mama Boko Haram

Hukumar yaki da rashawa ta EFFC, ta gurfanar da Aisha Alkali Wakil wanda aka fi sani da ‘Mama Boko Haram’ a gaban Mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun Jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri, a bisa sabbin tuhume tuhume guda uku da suka hada da damfarar kudi har N41,777,750.

An gurfanar da Mama Boko Haram tare da wani mai suna Tahiru Saidu Daura, da Prince Lawal Shoyede, shugabannin Complete Care and Aid Foundation (wata kungiyar sa kai).

A wata sanarwa da shugaban yada labaran EFFC, Wilson Uwujaren ya fitar, wa?anda
ake tuhumar ana zargin su da damfarar wata Hajiya Bilkisu Mohammed Abubakar akan kwangilar da ta haura miliyan 41 ga gidauniyar Complete Care and Aid Foundation, mallakar Wakil, amma suka ki biya.

An bayyana musu tuhumar kamar haka:
Aisha Alkali Wakil, Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyede a matsayin shugabannin Complete Care and Aid Foundation (kungiyar sa kai) wasu lokuta a shekarar 2018 a Maiduguri, Jihar Borno a wannan kotu mai albarka, ana tuhumar ku da ha’intar wata Hajiya Bilkisu Mohammed Abubakar ta Ihsan Vendor Services, da ta kawo muku kayan dakin gida, kayan wuta da kayan abinci na fiye da N34,593,000 (miliyan 34 da dubu dari biyar da 33) tare da umartar a kai kayan gidan shugaba/wanda ya samar da gidauniyar Complete Care and Aid Foundation(kungiyar sa kai) Aisha Alkali Wakil, laifin da ya sabawa sashe na 320 (a) kuma aka tanadi hukunci a sashe na 322 na kudin Penal Code na Jihar Borno.”

Sai dai wanda ake zargin sun karyata tuhumar da ake musu. A dalilin haka, lauyan masu kara, Haruna Abdulkadir, ya bukaci kotu ta saka ranar sauraron shaidu, don ba wa?anda ake karar damar daukar lauya.

Mai shari’a Kumaliya ya dage sauraren karar zuwa 26 ga Janairu 2021 tare da umartar ‘Mama Boko Haram’ da Shoyede da su dauki lauya, ko kuma aci gaba da sauraren karar da EFFC ta shigar ba tare da lauya mai kare su ba.

Exit mobile version