Borno: An Banka?o Ma’aikatan Bogi Dubu 22,556

Gwamnatin jihar Borno ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ta banka?o malaman bogi da ma’aikatan ?ananan hukumomin dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma’aikata da malamai da Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin aiwatarwa.

Al?aluman sun nuna kimanin ma’aikatan bogi 14,662 aka gano a ?ananan hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ?angaren ilimi.

Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar ku?i sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ?angaren malaman firamare ka?ai dake ?ananan hukumar 27 dake fa?in jihar.

Bayan kar?ar rahoton ne kuma gwamna Zulum, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkar ilimi a jihar Borno, kasancewar gwamnatinsa ta baiwa harkar ilimin firamare fifiko.

An fara tantance ma’aikata a jihar ta Borno tun a shekarar 2013 inda aka samo dubbanin ma’aikatan bogi. Gwamna Zulum ne ya yanke shawarar fa?a?a tantancewar har zuwa ma’aikatan ?ananan hukumomin jihar Borno guda ashirin da bakwai.

Related posts

Leave a Comment