Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Bola Tinubu Ya Karbi Shaidar Lashe Zabe Daga INEC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shaidar cin zaɓen 2023.

Shugaban Hukumar Zaɓen Ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya miƙa masa shaidar a Abuja.

Haka ma, shugaban na INEC ya bai wa mataimakinsa Kashim Shettima, shaidarsa.

An danka musu takardar shedar ne sa’o’i kalilan bayan da INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023, inda ya samu kuri’a 8, 794, 726, da suka ba shi galaba a kan sauran ‘yan takara 17.

A wani labarin na daban sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima sun kai ziyara ga shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura ta jihar Katsina.

A wani saƙo da babban mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da mataimakinsa na tare ne da wasu gwamnonin APC mai mulki yayin ziyarar.

Cikin gwamnonin da suka yi wa sabon shugaban ƙasar rakiya har da gwamnan Kaduna Malam Nasir EL-Rufai da gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Da asubahin ranar Laraba ne dai hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Exit mobile version