Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da yan bindiga idan har tana son tabbatar da tsaro a makarantu, da natsuwa tsakanin ‘yan Najeriya.
Rahotonni sun bayyana cewar tun a cikin watan Disambar 2020, yan bindiga sun sace dalibai a kalla so shida a makarantu da dama a yankunan arewa maso yamma da tsakiya inda suka sace a kalla dalibai da malamai 700.
Satar dalibai na baya-bayan nan ya afku a ranar Alhamis yayin da yan bindigan suka kai hari makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri, jihar Kebbi inda suka sace dalibai da malamai.
Satar daliban ya janyo an dakatar da makarantun kwana an kuma tura jami’an tsaro makarantu a wasu jihohi domin ceto ɗaliban da farauto ‘yan Bindigar.
Shawarar da Gumi ya bawa gwamnatin tarayya A yayin hirar shi da manema labarai ya ce hare-hare ta sama da sojoji ke kaiwa yan bindigan ba zai magance matsalar ba domin su kansu yan bindigan ‘fitina ce ta saka su abin da suke yi’.
“Idan ana son tsare makarantu, mai zai hana a tattauna da yan bindigan. A tattauna da su; ba su da yawa. Za ka iya kirga su da hannun ka. Makarantu nawa za ka tsare? Ba zai yiwu ba.
A dukkan arewa maso yamma, yan bindigan ba za su dara 100,000 ba. Wannan kaman digon ruwa ne a teku,” in ji shi. “Wadanda ke da makamai kenan; domin ba dukkansu ke da makamai ba. Kashi tamanin cikin dari na wadanda ke da makamai suna amfani da su ne don tsare shanunsu daga barayin shanu.
“Suma cikin fitina suke. Hare-haren sama da ake kai musu zai lalata lamarin ne domin idan ka fara kashe ‘ya’yansu, ka tuna ‘ya’yan mu na hannunsu.”