Boko Haram Ya Kamata Ku Tunkara Ba Zaben Ondo Ba – Zulum Ga Soji

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya shawarci Sojoji su rabu da shirin bayar da tsaro a zaben jihar Ondo na ranar Asabar, 10 ga Oktoba, su fuskanci ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabas.

Zulum ya bayyana hakan ne a taron babban hafsan Sojin Najeriya daya gudana ranar Talata, 6 ga watan Oktoba a Maiduguri, birnin jihar Borno. Zulum ya ce ya yi mamaki lokacin da Buratai ya ke alfaharin nasarar da Sojoji suka samu wajen bayar da tsaro a zaben gwamnan jihar Edo kuma suna shirin maimaita hakan a zaben jihar Ondo.

“Lokacin da babban hafsan Soji yayi magana da nasarar da suka samu a zaben Edo da kuma shirin na Ondo, abin ya ban tsoro saboda ina son Sojojin Najeriya su mayar da hankali wajen yakin yan ta’adda,”.

Zulum ya bukaci Sojojin su fara shiga lungu da sakon yankin domin sabawa da mutane saboda a yarda da su yayinda suke gudanar da ayyukansu. Ya yi kira ga Sojojin su kutsa inda ‘yan Boko Haram ke boye kuma su rika bibiya bayan kowani hari.

Ya jinjinawa Sojojin bisa namijin kokarin da sukeyi wajen kawar da ‘yan ta’addan. Ya ce wajibi ne ya yabawa Sojoji duk yayinda suka samu nasara kuma ya sokesu lokutan da sukayi kuskure.
Ya bukaci a hukunta masu yiwa kasa zagon kasa cikin Sojoji da fararen hula.

Labarai Makamanta

Leave a Reply