Boko Haram: Sauya Shugabannin Tsaro Ne Mafita – Mongono

Mai tsawatarwa na majalisar wakilai a Najeriya ya ?ora alhakin gazawar dakarun sojin ?asar na kawo ?arshen ya?i da Boko Haram kan rashin karsashin aiki saboda komai girman matsayin hafsa, ba zai kai ha?ura a mu?amin soja ba.

Mohammad Tahir Monguno ya ce matsalar ta janyo dakushewar tsimi da rashin kuzarin sojoji, wa?anda kuma ke shafar ya?in da Najeriya ke yi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

“Wa?ansu dalilan cikin rashin yin nasara a ya?in nan da ake yi ma, (akwai) sanyin jiki da kuma rashin kuzari na sojoji manya-manya wanda suna ganin ya kamata su ?ure (mu?aman aikin soja) amma ba su ?ure ba,”

Monguno na wannan jawabi ne yayin zantawa da BBC kan binciken da majalisar wakilan ?asar ke yi bayan sanar da murabus ?iin wasu sojoji 365 farat ?aya.

A cewarsa, ri?e wasu hafsoshi da gwamnatin ?asar ta yi na sanya manya-manyan sojoji a Najeriya kai wa shekarun barin aiki ba tare da sun samu damar da suka cancanci samu ba.

“Ai kowa in ya shiga aiki, kowanne irin aiki ka shiga, kana so ka je ka yi girma, ka ?ure, kafin ka sauka. Amma kana ganin wa?ansu sun ?ure, lokacinsu na murabus ya yi, ba su yi murabus ba. An ri?e su!
Kai, ba za ka iya ka ?ure ba, ka ga wannan zai rage kuzarinka. Zai rage kuzarin aiki,” in ji ?an majalisar.

An da?e ana kiraye-kiraye don neman sauya manyan hafsoshin sojin ?asar, ganin yadda rikicin Boko Haram da na ‘yan fashin daji suka ?i ci suka ?i cinyewa a wasu sassan Najeriya.
Rikicin na Boko Haram dai ya shafe tsawon shekara 11, kuma har yanzu ?ungiyoyin ‘yan ta-da-?ayar-bayan da suka rabu zuwa ISWAP da Boko Haram na ci gaba da kai ?azaman hare-hare a yankin Tafkin Chadi.

Ya ce ya gode wa Allah, don kuwa lokacin da gwamnati mai ci ta hau kan mulki, shi da kansa ba zai iya zuwa maza?arsa ta Monguno ba, saboda hatsarin da ke tattare da haka, amma yanzu an samu nasara.

Yanzu in na tashi zan iya zuwa Monguno. An yi nasara! Amma bayan an yi nasarar kuma, muka zauna, muka gani abin ya fara komawa baya”.

Wasu masharhanta a Najeriya dai na cewa ba sabon abu ba ne yin murabus ?in sojoji da dama, amma ‘yan majalisar wakilai sun ce ba a ta?a ganin irin haka ba a ?asar.

Ya ce wata?ila kwamandojin ne yanzu suka gaji, don haka ya nanata bu?atar neman cire manyan hafsoshin rundunonin sojin ?asar, don maye gurabensu da sabbin jini.

Ya nuna cewa ba daidai ba ne barin wa?ansu da lokacin murabus ?in ya yi, su ci gaba da aiki, yayin da na-?asa da su ke cimma shekarun barin aiki suna murabus daga aikin soja.

“Shi ya sa mu, muka ce ya kamata su hafsoshin ma, su tafi saboda mu samu ma ga wasu (da za su fito) su girma, kuma mu ga irin rawarsu,” in ji mai tsawatarwa.
Mu abin da muke gani ke nan, amma su kuma ?angaren zartarwa suna gani a lokacin ya?i bai kamata a canza kwamanda ba, cewar Monguno. “To amma in abin kullum yana komawa baya fa?”

?an majalisar ya ce kamata ya yi a canza su, ta yadda gwamnati mai ci za ta ?ora kan nasarorin da ta samu a ya?i da ‘yan ta-da-?ayar-baya.

Ya ce majalisar wakilai ta bai wa kwamitin da ke bincike kan murabus ?in ?aruruwan sojojin Najeriya tsawon mako guda don ya gabatar da rahotonsa.

Kuma a tsawon wannan lokaci, ana sa rai kwamitin zai gana da sojojin da suka sanar da yin murabus da kuma su kansu manyan hafsoshin sojin Najeriya har ma da ministan tsaron ?asar.

Monguno ya ce jazaman ne binciken ya tattaro shaida kan dalilan da ke janyo irin wannan yin murabus na ?umbin sojojin Najeriya tashi ?aya.

Shin lokacin murabus ?in su ne ya yi bisa doka? Ko kuwa akwai wa?ansu dalilai da ya sanya su barin aiki? ?an majalisar ya tambaya.

Related posts

Leave a Comment