Boko Haram: Sauya Shugabannin Tsaro Ne Mafita – Mongono

Mai tsawatarwa na majalisar wakilai a Najeriya ya ɗora alhakin gazawar dakarun sojin ƙasar na kawo ƙarshen yaƙi da Boko Haram kan rashin karsashin aiki saboda komai girman matsayin hafsa, ba zai kai haƙura a muƙamin soja ba.

Mohammad Tahir Monguno ya ce matsalar ta janyo dakushewar tsimi da rashin kuzarin sojoji, waɗanda kuma ke shafar yaƙin da Najeriya ke yi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

“Waɗansu dalilan cikin rashin yin nasara a yaƙin nan da ake yi ma, (akwai) sanyin jiki da kuma rashin kuzari na sojoji manya-manya wanda suna ganin ya kamata su ƙure (muƙaman aikin soja) amma ba su ƙure ba,”

Monguno na wannan jawabi ne yayin zantawa da BBC kan binciken da majalisar wakilan ƙasar ke yi bayan sanar da murabus ɗiin wasu sojoji 365 farat ɗaya.

A cewarsa, riƙe wasu hafsoshi da gwamnatin ƙasar ta yi na sanya manya-manyan sojoji a Najeriya kai wa shekarun barin aiki ba tare da sun samu damar da suka cancanci samu ba.

“Ai kowa in ya shiga aiki, kowanne irin aiki ka shiga, kana so ka je ka yi girma, ka ƙure, kafin ka sauka. Amma kana ganin waɗansu sun ƙure, lokacinsu na murabus ya yi, ba su yi murabus ba. An riƙe su!
Kai, ba za ka iya ka ƙure ba, ka ga wannan zai rage kuzarinka. Zai rage kuzarin aiki,” in ji ɗan majalisar.

An daɗe ana kiraye-kiraye don neman sauya manyan hafsoshin sojin ƙasar, ganin yadda rikicin Boko Haram da na ‘yan fashin daji suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a wasu sassan Najeriya.
Rikicin na Boko Haram dai ya shafe tsawon shekara 11, kuma har yanzu ƙungiyoyin ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka rabu zuwa ISWAP da Boko Haram na ci gaba da kai ƙazaman hare-hare a yankin Tafkin Chadi.

Ya ce ya gode wa Allah, don kuwa lokacin da gwamnati mai ci ta hau kan mulki, shi da kansa ba zai iya zuwa mazaɓarsa ta Monguno ba, saboda hatsarin da ke tattare da haka, amma yanzu an samu nasara.

Yanzu in na tashi zan iya zuwa Monguno. An yi nasara! Amma bayan an yi nasarar kuma, muka zauna, muka gani abin ya fara komawa baya”.

Wasu masharhanta a Najeriya dai na cewa ba sabon abu ba ne yin murabus ɗin sojoji da dama, amma ‘yan majalisar wakilai sun ce ba a taɓa ganin irin haka ba a ƙasar.

Ya ce wataƙila kwamandojin ne yanzu suka gaji, don haka ya nanata buƙatar neman cire manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasar, don maye gurabensu da sabbin jini.

Ya nuna cewa ba daidai ba ne barin waɗansu da lokacin murabus ɗin ya yi, su ci gaba da aiki, yayin da na-ƙasa da su ke cimma shekarun barin aiki suna murabus daga aikin soja.

“Shi ya sa mu, muka ce ya kamata su hafsoshin ma, su tafi saboda mu samu ma ga wasu (da za su fito) su girma, kuma mu ga irin rawarsu,” in ji mai tsawatarwa.
Mu abin da muke gani ke nan, amma su kuma ɓangaren zartarwa suna gani a lokacin yaƙi bai kamata a canza kwamanda ba, cewar Monguno. “To amma in abin kullum yana komawa baya fa?”

Ɗan majalisar ya ce kamata ya yi a canza su, ta yadda gwamnati mai ci za ta ɗora kan nasarorin da ta samu a yaƙi da ‘yan ta-da-ƙayar-baya.

Ya ce majalisar wakilai ta bai wa kwamitin da ke bincike kan murabus ɗin ɗaruruwan sojojin Najeriya tsawon mako guda don ya gabatar da rahotonsa.

Kuma a tsawon wannan lokaci, ana sa rai kwamitin zai gana da sojojin da suka sanar da yin murabus da kuma su kansu manyan hafsoshin sojin Najeriya har ma da ministan tsaron ƙasar.

Monguno ya ce jazaman ne binciken ya tattaro shaida kan dalilan da ke janyo irin wannan yin murabus na ɗumbin sojojin Najeriya tashi ɗaya.

Shin lokacin murabus ɗin su ne ya yi bisa doka? Ko kuwa akwai waɗansu dalilai da ya sanya su barin aiki? Ɗan majalisar ya tambaya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply