Boko Haram: Muna Cikin Tashin Hankali A Borno – Shehun Borno

Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi ya magantu kan hare-haren da ake kaiwa Shugabanni da al’ummar Jihar Borno, inda yake cewa ba wanda ya tsira daga hare-haren ‘yan ta’addar.

Basaraken yana magana ne kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna jihar, Babagana Umara Zulum yayin da ya kai wa Gwamnan ziyarar gaisuwar Sallah a fadar gwamnati da ke birnin Maiduguri, a yau Asabar.

A ranar Laraba ne aka kai wa jerin motocin gwamnan hari a hanyar garin Baga ta Karamar Hukumar Kukawa. An ga Gwamna Zulum a wani bidiyo lokacin da harin ke faruwa yana zargin sojojin da gazawa sannan daga baya ya zarge su da yin zagon kasa.

“Idan har za a iya kai wa babban mutum irin wannan hari, to ina tabbatar muku da cewa babu wanda ya tsira a jihar nan,” in Shehun

Ya ci gaba da cewa: Mai girma gwamna ba mu ji dadin abin da ya faru ba a Baga kuma wannan abun alhini ne.

Shehun ya nemi jama’a da su ci gaba da addu’a domin kawo karshen matsalar Boko Haram, wadda ta jawo asarar rayukan mutum fiye da 20,000 kamar yadda bincike ya tabbatar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply