Kungiyar gwamnonin arewa a ranar Laraba ta yi kira ga cibiyoyin tsaro da su binciki zargin da tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, ya yi na cewa “daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya”.
A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.
Takardar ta ce kungiyar, wacce ke aiki tare da gwamnatin tarayya, jami’an tsaro, yankuna, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da na addinai, don kawo karshen ta’addanci a yankin, tana bukatar bincikar ikirarin.
Ta kara da cewa: ” A matsayin mu na gwamnonin arewa, mun yi taruka babu adadi don tattaunawa a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa da kasar baki daya. Muna kushe duk al’amuran ta’addanci kamar Boko Haram, ‘yan bindiga, ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu.
“Muna saka jami’an tsaro da shugaban kasa don kawo karshen wannan matsalar.
“Cewa daya daga cikinmu yana jagorantar Boko Haram a Najeriya babban zargj ne wanda ba za mu bar shi haka ba. Muna bukatar a gaggauta bincike mai tsanani a kai.”
Kungiyar ta yi kira ga Mailafiya da sauran ‘yan Najeriya masu bayanai a kan ayyukan ta’addanci da kungiyoyinsu da su taimaka wa jami’an tsaro da gwamnati da bayanan don daukar matakin da ya dace.
Tana fatan wannan zargin ba salon kamfen bane ko kuma wani yunkuri ne na bata kokarin gwamnonin arewan wurin kawo karshen rashin tsaro a yankin ba.
Kungiyar gwamnonin arewa ta jaddada cewa ba za ta taba goyon bayan wani aikin ta’addanci ba, bayan harar daya daga cikin mambobinta da aka yi a kwanakin nan.