Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Za Su Zama Tarihi A Wannan Shekarar – Buhari

Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin shekarar nan ta 2021, za’a kawo karshen kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda, tare da neman ‘yan kasa su tallafawa rundunar soji da addu’a domin kai wa ga samun nasara.

Shugaba Buhari ya bayyana dalilai hudu da zasu ba gwamnati damar kawo karshen kungiyar Boko Haram a wannan shekara ta 2021.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ko kadan ba ya jin dadin ta yadda ake asarar rayuka a kasar tare da bayyana cewa nan bada dadewa ba za’a kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a faɗin ƙasar.

A cewar shugaban ƙasar Nijeriya za ta saka sadaukarwar jami’an soji a rai yayin yaki da ‘yan ta’adda domin ganin an ƙarar da su gaba ɗaya da shafe tarihin su a Najeriya.

“Za’a kara karfafa wa rundunar tsaro gwuiwa ta hanyar samar da kayan aiki da zasu basu damar murkushe ‘yan ta’adda, da kula da dukkanin bukatocin su domin samun galaba”.

“Hakazalika gwamnati za ta kara inganta tsarin walwalar jami’an tsaron da ke yaki da ‘yan ta’adda yadda za su fita daban da sauran jami’an tsaro domin tunkarar gagarumin aikin da ke gaban su”.

Daga ƙarshe Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su sanya jami’an tsaron cikin addu’o’i domin samun galaba a yaƙin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta