Boko Haram: Ɗaya Daga Cikin Gwamnonin Arewa Babban Kwamanda Ne – Mailafia

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Dakta Obadiah Mailafia, ya shaida cewar ya samu sahihin bayani daga wani dan Boko Haram da ya tuba da ke shaida masa cewar akwai gwamna a arewacin Nijeriya wanda dan Boko Haram ne.

Dakta Mailafia, wanda dan siyasa ne kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress a zaben da ya gabata ya shaida hakan ne a lokacin da ke bayani kai tsaye a gidan rediyon Nigeria Info Abuja 95.1FM a ranar Litinin.

Tsohon mataimakin gwamnan CBN din bai dai baiya sunan gwamnan da ke kan kujerar wanda ya zarga da cewar mambar Boko Haram ne ba.

Ya shaida cewar ‘yan ta’addan da suke arewa maso gabas da ‘yan bindigan da suke arewa maso yamma duk abu guda ne.

Ya shaida cewar wasu tubabbun Boko Haram ne suka shaida masa batun da ke cewa, “Sun shaida min cewa daya daga cikin gwamnonin arewa dan Boko Haram ne wanda kuma shi gwamanda ne ma ne Boko Haram a Nijeriya. Da ‘yan Boko Haram da ‘yan Bindiga duk abu daya ne, su na da nagartattun hanyoyin sadarwa da su ke tattaunawa.”

“Su na raba alburusai, kudade a sassa daban-daban na kasar nan,” Inji shi.

Shahararren dan siyasan ya kuma shaida cewar mai bashi labarin ya shaida masa cewar ‘yan Boko haram sun kuma shiga wasu sassan kudancin Nijeriya.

Ya dai nemi a dauki matakan da suka dace, yana mai cewa tabbas akwai matsalolin tsaro a Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply