Biyayya Ga Kundin Tsarin Mulki Ne Mafita Ga Shugabannin Afirka – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma a kan kar su kara wa’adin mulkinsu fiye da abinda kundin tsarin mulkin kasashensu ya ambata.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabin Najeriya a wurin taron ECOWAS na 57 da aka yi a birnin Niamey na kasar Nijar ranar Litinini.

Kazalika, Buhari ya shawarci abokansa su mutunta kundin tsarin mulkin kasashensu tare da gudanar da zabukan gaskiya.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin shugaba Buhari da kakakinsa, Garba Shehu, ya waallafa a shafukansa na sada zumunta.
“Yana da muhimmanci a wurinmu na shugabannin kasashen da ke zaman mambobi a ECOWAS mu kasance ma su biyayya ga kundin tsarin mulkin kasashenmu, musamman a kan wa’adin mulki.

Wannan batu ya dade yana haddasa rigingimu da tashin hankula a yankinmu.
“Mu na fuskantar kalubale da dama a wannan yanki na mu kuma bai kamata mu cigaba da haifar da baraka ta hanyar kara tsawon wa’adin mulki ba.
“Ina kira garemu; mu fi karfin zuciyarmu, mu fi karfin rudin maitar son makalewa a mulki fiye da wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanadar mana.

“Ina jinjina ga wadansu daga cikinmu da suka fi karfin zuciyarsu, tabbas tarihi zai cigaba da tunasu a matsayin jarumai a kasashensu da kuma yankin nahiyar Afrika ta yamma.
“Wani muhimmin batu da ke tare da wannan magana shine tabbatar da sahihin zabe na gaskiya, wanda ya yi daidai da zabin jama’a, akwai bukatar yin hakan kamar yadda ake da bukatar mutunta doka da tsari.”

Yayin taron na ECOWAS, shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma sun tattauna akan rikicin kasar Mali da kuma yadda za a tabbatar da cewa kasar ta koma kan mulkin dimokradiyya bayan wata 12.

Kazalika, shugabannin sun tattauna a kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasashensu da nahiyar Afrika ta yamma bayan sassauta dokar kulle da aka saka sakamakon bullar annobar korona.

Labarai Makamanta

Leave a Reply