Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana a kan binciken da ake wa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin zagon kasa (EFCC) Ibrahim Magu.
A wata takarda da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman a fannin yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar, yana bayanin dalilin da yasa ya aminta da dakatar da Magu.
“An samu korafi daban-daban a kan mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Bayan bincike na farko, an kira jami’an da ke karkashinsa inda aka bincikesu. “A saboda haka aka kafa kwamitin bincike mai kiyaye dokokin hukumar.
“A duk lokacin da ake zargin shugaban wata hukuma, a kan bukace shi da ya dakata da aiiki don a samu damar yin bincike ba tare da wata matsala ba.
“EFCC bata dogaro da yanayin mutum, a don haka bata sassauta wa kowa. Dakatar da Magu kuwa ya bai wa hukumar damar sauke nauyinta ba tare da wani cikas ba. “EFCC na da zakakurai, jajirtattun ma’aikata maza da mata masu fatan kiyaye dukkan dokokin kasar nan tare da mika duk wanda ya zo da almundahana gaban hukuma.
“Amma kuma, an bai wa Magu damar da zai kare kansa tare da amsa tambayoyin da ake masa. Hakan ce kuwa ta kamata a karkashin dokar kasar nan wacce ta bai wa kowa damar kare kansa,”.
Garba Shehu ya kara da cewa, dole ne a gane cewa yaki da rashawa a kasar nan ba a wuri daya ake tsayawa ba. Ta kowanne fanni ana kokarin tabbatar da shi.
Ya kara da cewa, masu kallon bincikar Magu da ake yi a matsayin wata koma baya ga yaki da rashawa, to a gaskiya sun kauce. Bincikar Magu na nuna cewa da gaske ana yaki da rashawa a bayyane ba tare da boye-boye.
A karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnati, babu wanda zai zamo zababben ko kuma wanda ya fi karfin hukuma, Magu bashi da wata kariya. Babu wata gwamnati a tarihin kasar nan da ta taba yin abinda wannan gwamnatin tayi na yakar rashawa karara.