Mukaddashin shugaban Hukumar NDDC masu kula da yankin Naija Delta ya tayar da bori a gaban kwamitin bincike na majalisar wakilai.
Wanda suke tuhumarsa da salwantar da fiye da naira biliyan ar’aba’in a hukumar tasa.
Jim kadan bayan gurfanar sa a gaban kwamitin don amsa tambayoyi, sai ya kife a kasa ya fara farfadiya. Nan take zaman ya tashi sakamakon hargitsi da aka samu.