Bayyanar Peter Obi Wajen Tarsiri Ta Haifar Da Surutai

IMG 20240321 WA0069

Rahotannin daga Suleja ta Jihar Neja na bayyana cewar a ranar Talata, 19 ga watan Maris aka gano tsohon gwamnan jihar Anambra a babban masallacin Suleja da ke kan hanyar Suleja zuwa Kaduna cikin jama’a yana sauraron tafsiri.

An ganshi yana zaune a sahun gaba cikin daruruwan musulmi, yana sauraren tafsirin Al-Kur’ani da limamin masallacin yake gabatarwa.

Wani ma’abocin dandalin X, @Imranmuhdz, ya wallafa bidiyon dan siyasar a lokacin da yake zaune a masallacin.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan bidiyo na Peter Obi kamar haka:

@OgaBossTweets ya ce: “Wannan neman suna ne da siyasa kawai. “Lallai wannan shi ne wasan wasa.”

@MA_Dibola ya ce: “Abin da ya rage masa shi ne ya tafi wajen bautar dodanni.”

@Fifa737 ya ce: “Idan Tinubu ne yake yin haka, za ku ce ba komai, amma idan Obi ne, sai kuce siyasa ce. Jama’a kar ku manta cewa dukkansu ‘yan siyasa ne.

@Abdul_charming ce: “Amma abin da yake yi bai yi yawa ba kuwa?” @AliyuSharif ce: “Ni fa na fara zargin wani abu.”

@plutoboy1990 ce: “Wannan shi ne abin da ya kamata ace kayi lokacin zaɓe.

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply