Bauchi: Za Mu Yi Ƙeƙe Da Ƙeƙe Wajen Biyan Albashi – Gwamna Bala

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed yace duk wanda yake da korafi na Albashi a fadin Jihar, yazo ayi Keke da keke, yace sun saka wuri a fadar gwamnatin Jihar, saboda akwai masu karbar albashin masu mataki na 15 maimaikom mataki na biyar 5

Gwamnan yayi furucin ne yau Asabar a karamar hukumar Gamawa a lokacin da yake rabon kayan tallafi na kimanin naira miliyan Hamsin (50) ga al’ummar yankin Katagum, a wani bikin cikar shekara biyu kankaragar mulkin jihar, domin rage masu radadin rashin sana’oi da aikin yi domin dogaro da kai.

Bala ya kara da cewa an cewa mun hana mutane albashi muna gina hanyoyi da masallatai yin hakan yana cikin alkawurran da muka dauka mu munzo gyara ne, ana korafi gwamnatin da ta ahude batayi aikin komai ba mu Kuma munzo muna aiki ana cewa bamu kyauta ba,

Ya kamata mutane su gane, “a lokacinmu bama zalunci magana na yanke albashi yanki fadi ne kawai idan akwai wani wanda baya samun albashi, Kuma da gaske hakane to an bude kujera ta musamman a fadar Gwamnati da ma’aikatar kudi, saboda abunda yake faruwa haka mutane suna sama da fadi da kudaden al’umma”ya fada.

Har’ila yau, yace,” yau ace albashin da Mike biya a Jihar Bauchi yafi na Jihar Kano masu dumbin al’umma, kana nan hukumomin su 44 su kimani mutum miliyan 15 munfi Kaduna yawan biyan albashi wanda suka fimu samun kudaden shiga, kudin albashinmu ya kusan na Jihar lagas, to kunsan cewa talakawan Jihar Bauchi ana cutan ku, nazo inyi gyara ne, inyi ma talakawa aiki, tare da ababen more rayuwa da tallafin gwana”.

Uwar gidan Gwamnan Hajiya Aisha Bala Mohammed wacce ta kasance a wajen taron ta gargadi wadanda aka basu tallafin da su ji tsoron Allah suyi amfani da kayan tallafin domin bunkasa rayuwarsu dana iyalansu,

Kayayyakin da aka raba a wajen taron sun hada da Baburan hawa, kirar Bajaj, Keken dinki, injinan markade, kayan sana’ar Masa da Kosai da kuma Dabbobi na kiwo, tare da kudade ga masu kana nan masana antu da yan kasuwanci.

Daga karshe Shugaban karamar hukumar Gamawa Alhaji Babayo Ahmad Maikasuwa, ya yabawa gwamnan kan irin ayyukan tallafi ma talakan Jihar da kayan more rayuwa domin ci gabansu da inganta rayuwa baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply