Bauchi: Za A Biya Alhazzan Da Aka Cuta Miliyoyin Kuɗaɗe

Hukumar Alhazan Jihar Bauchi ta bankado fiye da naira miliyan 74 na karya da aka karba ba bisa ka ida ba, a hannun mahajattan shekara 2019 a fadin Jihar, wanda gwamnati zata fara biyansu a cikin mako mai zuwa.

Shugaban hukumar Alh. Abubakar Babangida Tafida. ya shaida ma manema labarai a offoshin hukumar, cewa biyo bayan kafa kwamitin bincike da gwamnatin Bala Abdulladir Mohammed ta tayi tare da hadin gwiwar hukumar binciken cin hanci da rashawa ta kasa wato EFCC, suka samu wadan nan kudade na mahajjata.

Ya kara da cewa, Gwamnan Jihar Bala Mohammed tuni ya bada ummurni ga hukumar Alhazan ta gaggauta biyan wadanda abin ya shafa, da akaso a chucesu a aikin hajji 2019, inda ya kara da cewa ranar Litinin za a fara biyansu kudaden a dukkanin kana nanan hukumomin Jihar guda ashirin.

Babangida Tafida, yace “akwai amirul hajji da mataimakinsa a dukkanin kana nan hukumomi su zasu yi wan nan aikin biya, tare da cika ka’ido jin da hukumar alhazai ta shimfida, saboda haka muna kiran duk wanda yake da hakki a hukumar alhazai to ya garzayo ranar Litinin mai zuwa nan 14 ga watan Disamba 2020”

Kana ya kara da cewa “wadan da sazu karbi kudaden sun kai su kimanin dubu daya da dari shida da hamsin 1,650 daga kana nan hukumomi ashirin na Jihar”

Bugu da kari, Tafida ya ce wadan nan mutane da suka aikata wan nan badakala na zunzurutun kudadin al’umma, sun amince da tuhumar da ake masu, kuma suna hannun hukumar jami’an tsaro ana ci gaba da tattara bayanai don yi masu hukuncin da ya dace dasu.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply