Bauchi: Za A Ƙwato Filayen Kiwon Da Aka Handame A Misau

Sabon kantoman karamar hukumar Misau Alhaji Isa Kufai, yace zai kwato filayen kiwon da wasu mutane suka handame, inda rikici ya barke har da rasa rayuka da jikkata wadansu a kwanan baya.

Shugaban ya fadi hakan ne a zantawarsa da manema labarai kan wan rikici da kuma matakan da hukumar sa ta dauka.

Shugaban yace sun dauki matakin ne don kar wani abu mai kama da haka ya sake aukuwa a yankin kauyen Zadawa na karamar hukumar Misau, inda yasha alwashin duk wanda ya shiga hannun hukuma kan wan nan rikici to ya kuka da kansa.

“Na shigo na samu wuri wanda yake cikin rudu, rudun abubuwan da suka faru na dar-dar, shine tun zuwa na, nayi mitin da jami’an tsaro da suwagabbanin addini dana alkalai da sarakuna muka tattauna yadda zamu dakile kara faruwar wan nan rikici”.

Ya ci gaba da cewa “mun zagaya dukkan gidajen da aka samu wan nan rigima da wanda aka kashe ko aka ji masu ciwo munyi ta aziyya”

Kana shugaban ya kara da cewa, “mutane sun san muhimanci dazuzzukan, yace duk korafin da muka samu mutanen da suka je suna noma a filayen mun sami sunayensu, zamu gaya masu wan nan ba filin noma bane su tashi su nemi filin noma, duk wanda ya saya yayi asara ne bashi da hurumin shiga gandun dajin,

Isah Kufai, ya ce gwamnatin tarayya ce ke da hurumin bada fili a wurin, abun da bai taba faruwa ba a jihar Bauchi, yau ya faru kar ka manta irin haka ya faru a jihar zamfara, sokoto da sauransu, baza mu bari ba, muna yine don kare lafiyan kowa da martaban makiyaya da manoma”.

Indai ba a manta ba gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed, ya dakatar da mai martaba sarkin Misau a karagar mulki, tare da shuwagabannin karamar hukumar Misau, har sai kwamitin da aka nada sun gama bincikensu kan wan nan rikici da kuma cimma matsaya.
##

Labarai Makamanta

Leave a Reply