Bauchi: ‘Yan Jarida Sun Ƙaurace Wa Ɗaukar Labarin Mataimakin Gwamna

‘Yan’Jarida masu dauko rahottani a Jihar Bauchi sunce bazasu sake wata alaka da mataimakin Gwamnan Jihar ba sanata Baba Tela kan rashin mutunta aikin Jarida

Kungiyar ta cimma matsaya ne a wani taro na gaggawa da ta kirayi
yayanta jim kadan bayan dawowar su daga takaitaccen taron manema labarai da aka gayyace su a offishin mataimakin Gwamnan Jihar.

Kana kungiyar tace sun tafi offishin ne bisa gayyatar da bangaren sadarwa na offishin gidan gwamnati tayi musu, amma a cewarsu abun mamaki da shigowar mataimakin Gwamnan Sanata Baba tela sai ya kada baki yana cewa, su fita daga dakin taron ba a bukatansu anan, ba tare da tausasawa,

Wan nan abu yayi matukar bata ma manema labaran rai, tare da fusata su, har takai ga daukan wan nan mataki, a cewar kungiyar Yan’jarida, suna da daraja ta daya a duniya, bama a Jihar Bauchi kawai ba, saboda haka bazasu lamunci kaskantarwa ba ko aworin waye, kuma babu nadamar yanke wan nan hukunci.

Sakataren kungiyar masu dauko rahotannin, Samuel Luka a wata takarda da suka tura kafafen watsa labarai na ciki da wajen Najeriya, inda yace sun dauki matakin ne don ya zama ishara ga wasu masu rike da madafun iko a kowani mataki na shugabanci.

Ya kara da cewa abun Kuma ya faro ne a gaban wadansu masu ruwa da tsaki na Jihar, wadanda sukazo wajen taron, da zasu yi a offishin mataimakin Gwamnan, inda suma maganar batayi masu dadin sauraro ba.

Bugu da kari kungiyar tace an jima ana ma Yan’jarida kallon hadarin kaji, wadanda kuma masu madafun ikon suke tunkaho dasu, kuma da bazar manema labarai suke taka rawa, don cimma muradunsu.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta