Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Yi Kiran Shayar Da Ruwan Nono Zalla

Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Mohammed ta gargadi matan jihar kan su tabbatar da sun bayar ma jariransu ruwan no-no zalla na tsawon wata shida don samun kariya daga daukan chututtuka.

Tayi wan nan gargadin ne a lokacin kaddamar da bikin shayar da nono na mako guda da ake gudanarwa a fadin duniya, wanda ayau akayi bikin na bana a cibiyar bada maganin kiwon lafiya a matakin farko dake yanki Miri a garin Bauchi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Hajiya Aisha ta yaba da kokarin hukumomi domin fadakar da mata masu shayarwa da masu juna biyu, kan al’amarin kiwon lafiyarsu dana yayansu, ta kara da cewa ya kamata mata su koyi amfani da KuNu mai sinadarin karin kuzari ma jariransu wanda akafi sani da suna (Turnbrown) a turance, wadda ake hada wa da Waken Soya, Gyada, Dawa, Kwai, Man-ja, da sukari daidai dandano.

Haka taja hankalin hukumar lafiya a matakin farko na jihar dasu tabbatar an cigaba da wayarma da mata kai musamman masu shayarawa a cikin al’umma, tare da mutanen karkara.

A yayin bikin kwamishinan lafiya na jihar Dr. Aliyu Maigoro wadda aka wakilce shi a wajen taron, yace babban mataki shine hadin kai daga iyaye da sauran masu ruwa da tsaki don a gudu, a tsira tare ta fanin kiwon lafiya, ya kuma ce tuni hukumar lafiya a matakin tarayya ta bada izinin amfani da sinadari na rukunin ‘A’ domin kariya daga daukan chuta da kuma rage mutuwar mata masu juna biyu.

Shima anashi tsokacin shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko na Jihar Dr. Rilwanu Mohammed ya jaddada bukatar dake akwai ga mata su cigaba da amfani da abinci mai gina jiki, kuma ya kirayesu da su kara himmatuwa da tsaftace hannayensu baki daya domin kare kai daga chututtuka.

Suma masu ruwa da tsaki a harkokin kiwon lafiya a wajen taron, (WHO, UNICEF Bill and Milendagate,) sunyi la akari da wan nan mako na shayar da no-no uwa, cewa lokaci ne mai muhimmaci ga mata masu shayar da no-no, kana da kuma hadin kai na zahiri.

Kuma suka tabbatar da samun kariya a dalinkin shayar da no-no na tsawo wata shida kafin a fara basu ruwa da sauran kayan abinci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply