Uwargidan Gwamna Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed ta sharwaci Malamai a dukkan fadin Jihar Bauchi da su rika karantar da tarbiyar aure ga maza da mata, a wani mataki na rage yawaitar fadace-fadace daka iya jawu rabuwa a tsakanin ma’aurata.
Tayi wan nan furucin ne a ranar Jumma’a a wani taron addu’a data kira wanda aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnatin Jihar Bauchi. Tare da kaddamar da kwamitin kula da yawan cin zarafin mata da yara a fadin Jihar baki daya
Aisha Bala tace yawan mutuwar aure yayi yawa a cikin al’ummar musamman a kasar hausa saboda karancin sanin hakin dake rataye a wuyan ma’aurata, ta Kara da cewa Allah ya riga ya shimfida ka’idojin aure don haka kowa na da hakkin ilmantar da wadanda zasu yi aure tun kafin lokacin yayi.
Ta kara da cewa Allah ya riga yayi ma sha anin sure albarka, saboda haka yana da kyau kowa ya san matsayin sa tare da hakkokin fake ciki, kana da yin addu’a ma ma’uratan dasuyi hakuri su zauna in akwai matsala su shirya a tsakaninsu, ba sai sun bari anji kansu ba, a cewarta hakuri shine komai a rayuwa.
Har’Ila yau Aisha ta bukaci kwamitin Hana cin zarafin mata da yara kanana, dasu jajirce Kan aikinsu saboda aiki ne na na samun mafaiat daga wan nan mummunar dabi’a, na fyade ma manyan Mata da yara masu karancin shekaru tace wan na rashin imani ne, don haka duk Wanda suka kama dole ne su fuskanci shari’a tare da hukunci mai tsanani.
Ana shi jawabin mukaddashin Mai rikon kujerar Shugaban ma’aikatar kula da mata da ci gaban yara, Alhaji Ibrahim Aliyu yace tuni kwamitin ta shiga aiki gadangadan inda suka sami nasarar chafke wadanda suka aikata fyade kimani Hamsin da bakwai 57 a wurare dabam dabam, sannan kwamitin sun samar da wurin sake tsugunar da wadanda wan nan bala’i na fyde ya rutsa dasu.
Kana yace ya jinjina ma Uwargidan Gwamnan kan kokarinta na ganin an kawo karshen fyade da sauran laifuffuka dake alaka da matsalar cin zarafin mata kai tsaye tare da kiran mambobin kwamitin da suyi aikinsu ba sani ba sabo.
Malamai da dama a wajen taron sunyi nasiha tare da jan kunnen iyaye da ma masu son yin aure da su ci gaba da neman ilimin zamanta kewa da kuma na hakkokin aure don kaucewa rikita rikita da rashin jituwa domin aure abune mai muhimmanci a rayuwan dan Adam.