Bauchi: Tsangayar Almajirai 53,000 Da Yara Mata Sun Samu Kayan Karatun Zamani

Kimanin Al’majirai da yara mata su 53,000 a Jihar Bauchi suka sami kayan karatu irin na zamani, domin farfado da ilimin yara musamman karatun yara mata, a karkashin wani shiri na bada kyakkawan ilimi ga dukkan yara kana na (BESDA) a fadin jihar.

Shugaban hukumar karatu a matakin farko na jihar Dr. Abubakar Sirimbai Dahiru Bauchi, ya fadi hakan ma manema labarai jiya yayin da yake zagayawa don ganin yadda rabon kayan ke wakana a kanan hukumomi tara na jihar.

Yace kayan da aka raba sun hada da littafin karatu, kayan sawa na makaranta, kujeru, jakan makaranta, kayan kula da lafiya, kayan wanka, da kuma kekunan masu bukata ta musamman a makarantun allo da yara mata.

Ya kara da cewa a karkashin shirin an gina makewayi irin na zamani rumfan karatu da kuma rijiyan burtsatse domin samar da ruwa a kankari a makarantun

Sirimbai yaci gaba da cewa “rabon kayan katatun yazo daidai lokacin da tuni an dauki malamai 1,500 da zasu karantar a sabbin cibiyoyin da aka bude domin karatun tsangaya da yara mata sun dawo haikan”.

Yace “duk yaron da bai karbi nasa ba, zai samu nashi nan ba da dadewa ba saboda, acewarsa chutar korona ce ta kawo tsaikon shirin a baya, “a yanzu haka muna da yara su 58,000 a wadan nan kanana hukumomin da suka dawo makaranta yayin da aka sake budewa, saboda haka mun wuce yawan da ake bukata tun a farkon shirin” ya fada.

Shugaban yace kananan hukumomin sun hada da Alkaleri, Bauchi, Misau, Ganjuwa, Jama’are, Itas/ Gadau, Katagum, Zaki, da kuma Gamawa.

Wasu daga cikin Malaman yaran, Alaramma Malam Kabiru da Malam Muhammad Zirame sun yaba da hubbasan hukumar rabon kayan kan irin na mijin kokarinsu don ganin sun cire ma marasa galihu kitse a wuta ta fannin neman ilimin zamani dana muhammadiyya.

Sun tabbatar da cewa zasu himmatu ta ganin yan makarantan sunyi amfani da dukkanin kayayakin karatun da aka basu domin inganta ilimimsu, da kuma na karatu yara mata wanda yafi samun koma baya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment