Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci manyan malamai na kungiyar Izala zuwa Bauchi domin nemawa Sheikh Idris Abdulaziz sauki a shari’ar da ake ta zarginsa da tayar da hankalin jama’a.
Fintiri tare da shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarenta Sheikh Kabiru Gombe da kuma wani malami mazaunin Kano Sheikh Abdulwahhab sun gana da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad.
Babban sakataren yada labarai na Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya tabbatar wa majiyarmu ganawar, inda ya ce gwamnan ya gana da takwaransa na Bauchi domin sasanta al’amarin tsakanin gwamnatin Bauchi da Sheikh Idris.
Sheikh Idris, wanda aka sake a ranan ya kasance a gidan yari sama da kwanaki talatin bayan da alkalin kotun shari’a da ke sauraron karar ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi. Malamin dai ya yi wasu kalamai ne akan Annabi Muhammad SAW da wasu malamai da dama ke kallon su a matsayin cin mutuncin ga ma’aiki, inda shi kuwa ya musanta aikata ba daidai ba.
Wani malami a Kano, Baffa Hotoro wanda ya goyi bayan Sheikh Idris ya shiga hannun jami’an tsaron farin kaya (DSS) a Kano saboda ya maimaita kalaman Sheikh Idris. A gefe guda, wasu ’yan daba sun kashe wani mutum kwanan nan a Sokoto bisa zarginsa da irin wadannan kalamai na Sheikh Idris. Sai dai, wasu na ganin akwai ‘yar tsama a tsakanin gwamnan na jihar Bauchi da Sheikh Idris, wanda aka ce hakan ne ya jawo tsare shi.