Bauchi: Sarkin Bauchi Ya Yi Gargadi Kan Rabon Tallafin CORONA

Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, kuma shugaban rabon kayan tallafi na annobar korona a jihar Bauchi, ya gargadi Sarakuna da Jami’an tsaro kan duk wanda aka kama ya karkatar da kayan tallafin zai dan dana kudarsa.

Sarkin yayi wan nan gargadin ne lokacin da aka fara rabon kayan tallafin a farfajiyar dakin ajiye kayayyakin gwamnatin jiha daura da Otal din Zaranda, zuwa kananan hukumomi bakwai 7 a fadin jihar.

Sarki Rilwanu Sulaiman, ya ci gaba da shaidawa manema labarai cewa “kimanin buhun hunan na kala kalan kayayyakin abinchi 29,500 za a rabasu zuwa kana nan hukumomin Bogoro, Dass, Darazo, Dambam, Ningi, Misau da kuma Jama’are”

Inda ya kara bayani da cewa “Abincin sun hada da shinkafa, Wake, Garin-Masara, Gero, man-Gyada, Gishiri, dunkulen Maggie, Sukari da dai sauransu” ya fada.

Ya kuma ja hankalin yan siyasa da masu sauratun gargajiya cewa, gwamnati tare da kwamitin alhakin rabon kayan baza su lamunci duk wani wanda yayi anfani da matsayinsa wajen rabon kayan, za susa kafar wando daya dashi.

Sarkin Bauchin ya sha alwashin sanya idanu sosai dun ganin kayan ya kai wajen talakawan da suka fi bukatar kayan tallafin, a yankin kana nan hukumomin jihar don rage radadin cutar korona da ta addabi al’umma.

Kana ya karkare da bayanin cewa, kawo yanzu babu wani labarin karkatar da kayan, tun lokacin da aka fara rabon a cikin makon jiya.

Da kuma kira ga masu hannu da shuni, da manyan kungiyoyi masu zaman kansu da suci gaba da tallafa ma marasa galihu a cikin al’umma baki daya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply