Bauchi: Rabon Tallafin Ambaliyar Ruwa Ya Bar Baya Da Ƙura

Gwamnatin Jihar Bauchi ta raba kayan tallafi na ambaliyar ruwa da cutar mashakon numfashi ga mutane dubu uku da dari biyar 3,500 a karamar hukumar Warji, inda matasan gari sukayi warwason kayayyakin tallafin

Jim kadan ne da barin mataimakin gwamnan Sanata Baba Tela wanda shine ya wakilci gwamnan jihar a wajen rabon kayan, matasan sukayi kukan kura, na in bakayi bani waje, sukayi dai-dai da kayan abincin kafin Jami’an tsaro su farga matasan sunyi abinda suke so.

In ba a manta ba, a kwanan baya ne ruwan sama yayi ambaliyar da yayi sanadiyar asarar rayukan mutane biyar da dukiya mai dumbin yawa a karamar hukumar Warji dake cikin jihar Bauchin, inda gwamnan yakai ziyarar ganin irin asarar da aka tabka a sanidiyar ambaliyan, tare da jajanta masu.

Ana shi tsokacin mai martaba Sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu wanda shine shugaban rabon kayan tallafin na jihar na Covid-19 wanda Alhaji Bala Kariya ya wakilce shi ya tabbatar da cewa rabon zai kai wajen mabukata ne kawai.

Hakimin garin warjin Alhaji Hassan Ismaila
Wanda shi akaba hakin karbar kayyakin, yace zasu kokarinsu don raba kayan abincin ga wadan fa ibtila’in ya shafa. da kuma sauran mabukata a yankin nasu.

Ayayin da yake mika godiyarsa ga mahukunyan jihar kwamishinan kana-nan hukumomi da masarautun gargajiya Abdurazak Nuhu Zaki
wanda yayi godiya a madadin wadan da aka kawu wa daukin kayan abincin, kana ya godewa gwamnan jihar kan jajircewar ganin sai an raba tallafin ga masu tsana nin bukata.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta