Daga Adamu Shehu Bauchi
Alhaji Nuhu Ahmed Wabi ya zama Sarkin Jama’are na Goma 10 biyo bayan tabbatar dashi da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi yayi a matsayin Sabon Sarkin a ranar litinin 28 ga watan faburairu
Wan nan tabbatar da shi kuwa tana kunshe ne a wata takarda da Gwamnan ya saka hannu kuma aka mika ma manema labarai a Jihar Bauchi hakan ya biyo bayan rasuwan tsohon sarkin Jama’are Alhaji Mohammed Wabi III Wanda shine mahaifin wanda aka nada a yanzu.
Tsohon Sarkin dai ya rasu ne bayan yasha fama da dogowar rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru tamanin da Uku 83 a duniya, kana ya share kimanin shekaru Hamsin 50 a karagar mulkin Masarautar Jama’are, inda ya zama Wanda yafi dadewa akan kujerar mulki na gargajiya a arewacin Najeriya.
A lokacin mika mashi wan nan takarda ta tabbatar mashi da sarautar, sakataren gwamnatin Jihar Ibrahim Kashim ne ya wakilci Gwamnan Bauchi a wajen mika mashi takaradar, inda ya shaida cewa Babu shakka anbi dukkanin wasu kaidoji na nada Sarki wanda masu zaban Sarki a Yan’majalisar masarautar suka mika sunayen wadanda suke nema, akarshe Allah ya bashi wan nan mukami
Gwamnan ya kirayi Sabon Sarkin da ya Riki aikinsa da gaskiya da rokon Amana, da Kuma mutunta mutanensa da mutuncin masarautar Jama’are ba tare da nuna ban banci ba
Bala yace Sabon Sarkin ya gaji ma haifinsa ne, don haka ana mashi fatan alheri da ya yayi abunda babansa ya yayi a lokacin mulkinsa ko kuma ya dara na Baban nasa
Kana Gwamnan yayi mashi Myrna da addu’an samun zaman lafiya da yalwar arziki a masarautar Jama’are da daukacin Jihar Bauchi dama Najeriya baki daya.