Bauchi: Mun Yi Wa Dogara Riga Da Wando – PDP

Jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi tace sunyi ma tsohon kakakin majalisar tarayya Honarable Yakubu Dogara riga, da wando, harda yar ciki don haka, ba abunda zai hana ta cin zabe.

Mai magana da yawon jamiyyar PDP na jihar Bauchin Alh. Yayanuwa Zainabari ya shaida hakan a yayin zantawarsu da Wakilin ‘Muryar Yanci’ a jihar Bauchi kan wan nan batu.

Kakakin yace, a yanzu ina tabbatar da cewa fitan Dogara Jamiyyar PDP ba a zalunce shi ba, a gwamnatance ba a zalunce shi ba duk abinda za ayi dashi ake yi a jamiyyance.

Zainabari ya ci gaba da karin bayani “mu muna tabbatar da cewa hatta matsayin kansila ba’ayi kansila na wan nan yankin ba saida mai girma gwamna tare da shugaban cin jamiyya suka tuntube shi, ya amince da abinda akayi, mene ne damuwansa, PDP ba abinda bata yi masa ba, ya fice ne don radin kansa, ya kamata mutanen yankinsa su san da haka”

Bugu da kari “Kuma biri yayi kama da mutum a dubu biyu da shabiyar 2015 a Jamiyyar APC yaci zabe suka yi mashi bita da kulli, suka hana shi tikiti, mutum hudu sun jima suna bauta wa jamiyyar PDP amma aka danne su akabashi dama shikadai ya tsaya, kuma wan nan bashine karo na farko ba da aka bashi dama, wan nan shine karo na ukku kenan a PDP, kuma babu shakka hakan yayi daidai da abin da ake fada cewa yayi hakane don gujewa ‘efcc’ da kuma maganan da ake cewa an kwadai ta mashi, Bola Ahmed Tinubu zai dauke shi a mataimakin shugaban kasa, a zaben 2023, a matsayinsa na dankasa ya fita ne don bukatar kansa”

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply