Bauchi: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya reshen jihar Bauchi sun gudanar da zanga zanga lumana don kawo karshen rashin tsaro da ya addabi yankin arewan baki daya.

Kungiyoyin sun gudanar da hakan a fadar jihar zuwa gidan gwamnati, bayan kiran uwar kungiyar data yi a jihohin arewa su goma sha tara (19) tare da kiran shugaban kasa da ya kara matsa kaimi kan yaki da tabarbarewar tsaro musamman a arewacin kasan.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Bauchi, Bello Aminu ya kara da cewa al’amarin tsaro sunyi kamari a yankin don haka hukumomi su tashi tsaye domin mutane suna cikin zullumi a ko daushe.

Kana ya kara da cewa, “Muna son gwamnati ta kara daukan jami’an tsaro tare da basu kayan aiki na zamani, sa anan ana haka wasu suna kira a wai a kawar da bangaren yan SARS mun goyi bayansu, gwamnati ta kawardasu, to me suke nema kuma,

“Mu bamu yadda da hakan ba, akwai makarkashiya a wan nan kira na kawar da bangaren sas, muma yanzu mun fito domin muna bukatar tsaro a yankin arewacin kasan nan, bamu san suwa suka sasu ba” ya fada.

Kana ya kara da kiran masu ruwa da tsaki a bangarorin al’umma da su taimaka ma gwammati ta ganin an samu tsaro mai inganci domin walwala jama’a da yelwar arziki a yankin arewacin Najeriya.

Yace dama yaya, balle kuma ace an rage ma jami’an tsaron na yan’sandan Najeriya karfi, mu muna goyon bayan kara masu karfi ne, da kuma daidai ta su a kan hanya su fiskanci ayyuka yan ta’adda, yan fashi da makami, garkuwa da mutane, fyde da dai sauransu.
#

Labarai Makamanta

Leave a Reply