Bauchi: Kungiyar Izala Ta Horar Da Matasa Sana’ar Dogaro Da Kai

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa’Ikamatus Sunnah karkashin Jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta horas da matasan yankin Arewa maso gabas sana’o’i domin du dogara da kansu.

Taron bada horon ya guda ne a jihar Bauchi inda ala koyawa matasan yadda ake hada sabulu da manshafawa da man wanke gashi da sauran kayayyakin kamshi da na girki.

Shugaban kungiyar Sheikh Bala Lau ya bayyana cewar burinsa ne yaga matasa suna samun dogaro da kansu domin rufawa kansu asiri. Ya kuma kara da cewar kungiyar zata cigaba da koyawa mutane sana’o’i daban daban a dukkan sauran Sassan Najeriya domin tallafawa inganta rayuwar matasa.

Sanata Yahaya Gumau shi ne ya wakilci shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan a wajen wannan biki ma yaye matasan da suka koyi sana’o’i. Ya jinjinawa kungiyar akan wannan yunkuri nata na ganin ta bunkasa rayuwar matasa ta hanyar nuna musu yadda zasu dogara ga kawukansu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply