Mutane manoma 18 ne aka tabbatar da sun riga mu gidan gaskiya a yammacin ranar Alhamis, mutum biyar 5 kuma sun jikkata a dalilin hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Itas/Gadau na Jihar Bauchi
Kakakin Yan’sanda na Jihar Bauchi DSP Ahmed Wakil shine yatabbatar ma da manema labarai aukuwar wan nan lamari, a kunshe a wani sako da ya fitar a daren Jumma’a.
Sakon ya ciga ba da cewa wan nan mummunan hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da manoman suke kan hanyar su na zuwa gona inda suka makare kwalekwalen dam a cikin kogin wanda ya jawo sanadiyar jirkicewa a yayin da suke tafiya a kogin Buji.
Rahoton ya ci gaba da cewa a halin da ake ciki tuni anyi zana’idan wadanda suka rasa rayukansu, mutum biyar kuma suna kwance a babban asibitin Itas/Gadau suna karbar magani.
A cikin wadanda hatsari ya ritsa dasu akwai yara su takwas 8 da kuma matasa su takwas 8 da manyan magidanta su biyu 2, kamar yadda mai unguwar garin ya sanar da jami’an tsaro a yankin Itas/Gadau.
Bugu da kari tuni gwamnatin jihar ta tura tawaga jami’an gwamnati domin tantance yadda al’amarin ya auku, da kuma jajen rashin rayukan da akayi ga iyalen mamatan.
Daga Adamu Shehu Bauchi