Bauchi: Gwamnati Za Ta Kashe Miliyan 759.5 Ga Jami’an Tsaro

Gwamnatin Jihar Bauchi zata kashe makudan kudade kimanin naira Miliyan 759.5 wajen sayo motoci na jami’an tsaro a dukkan fadin Jihar don dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da yan bindiga dadi.

Kwamishinan kudi na Jihar Umar Sanda Adamu ya shaida hakan, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta Jihar da tayi a ranar Alhamis, biyo bayan cimma matsaya kan tun karar hidimar tsaro dake addaban yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamishinan yaci gaba da cewa in har aka sayo motocin zasu taimaka sosai a hidimar bada tsaro a wuraran da suke da wahalar shiga cikin su sosai.

Tun a farko dai taron wanda gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Mohammed ya shugabanta, shine zamar majalisar karo na goma sha daya kuma na karshe a shekarar 2020.

Umar Sanda har ila yau ya fada cewa duk da dai Jihar Bauchi an santa da zaman lafiya, kuma tafi sauran jihohin kwanciyar hankali in aka kwatanta ta da sauran jihohin arewa maso gabashin kasan.

A cewarsa gwamnatin Jihar baza tayi kasa a gwiwa ba, kan kudurori na bada tsaro ga daukacin al’ummar Jihar baki daya, ya kara da cewa Jihar Bauchi bata samu tallafin motoci na tsaro ba guda ashirin da hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriyar, da ta raba ma sauran jihohin yankin.

Bugu da kari, yace jami’an tsaro sun roki gwamnatin Jihar ta saya masu motocin, domin zirga zirga a fadin Jihar, biyo bayan cire Jihar a matsayin wance zata mori tallafin motocin tsaro tun a farko, yace laakari da muhimmancin tsaro, gwamnan Jihar ya yanke shawarar a fara sayo guda hamsin 50 Wanda kudin kowane daya ya kai miliyan sha biyar 15. Inji kwamishinan kudi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment