Bauchi: Gwamna Bala Ya Kori Shugaban Hukumar Alhazzai

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya tabbatar da dakatar da Shugaban hukumar Alhazai na Jihar Bauchi Alhaji Abubakar Babangida Tafida daga aiki, Kuma na hannun damannsa, tare da bashi umarnin mika ragamar jagoranci hukumar a hannun babban ma’aikaci a hukumar nan take.

Sanarwar wadda ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, kana aka turama manema labarai, mai dauke da sa hannun mai bama gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai, Kwamred Mukhtar Gidado

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka aike ma da shi Babangida Tafida wan nan takadar dakatarwar ba tare da wani bata lokaci ba, da kuma bashi umarnin ya mika dukkan jagoranci hukumar zuwa ga hannun babban ma’aikaci a hukumance

Har, ila yau takardar tayi nuni da cewa zai ajiye aikin ne har sai an kammala binciken kwakwaf a aikin gudanar da hukumar wanda gwamnatin Jihar ta kaddamar.

Wan nan dakatarwar za iya cewa yazu da mamaki ganin yadda Shugaban hukumar Alhazan suke dasawa da gwamnan, kuma jigo ne a tafiyar Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar.

Masu iya magana dai sun ce ruwa baya tsami banza, Kuma lokaci ne kadai zai tabbatar da ko meke faruwa a hukumar Alhazan, har takai ga dakatar da shugaban, wanda ake ganin na hannun daman gwamnan ne a siyasance.

Related posts

Leave a Comment