Gidauniyyar ‘Haidar Care’ ta raba kayan abinci ga talakawa, marayu da marasa galihu a jihar Bauchi domin bukukuwan Sallahr layya.
Yayin raba kayayyakin abincin ga mabukatan, wanda ya gudana a farfajiyar Babban Masallacin garin Bauchi, jami’in tsare-tsare na gidauniyyar Muhammed Mukhtar Isa, yace tallafin abincin sunyi shine domin cire ma wadanda basu da wani katabus kitse a wuta, musamman ta fuskan abinci a yayin shagulgulan Sallah Babba,
Kana ya ce, wan nan yunkuri da hubbasa ne na gidauniyar domin taimaka ma wadanda basu da abincin da zasu sa abakin salati musamma a irin wan nan lokaci da ya kamata a ce musulmi na farin ciki a yayin bikin Sallah, haka nan a wajen taron ya nuna rashin jin dadinsa rare da zargin gwamnatoci da shuwagabbani da masu hannu da shuni, da barin talakawansu a cikin yunwa da kuncin rayuwa.
Bugu da kari, ana ta tsokacin wata jigo a gidauniyar Mariya Bappa Yari, ta fadi cewa wan nan taron jin kai ne da suka shirya shi domin rage ma marasa galihu radadin talauci, tare da mabukata a cikin al’ummar jihar, domin su samu abincin da zasu ci, harda makubtansu a lokacin bikin Sallah
“Abun takaici wadansu suna nan da abinci a runbun ajiyansu, amma har sai ya lalace alhali ga ma bukata suna ta maula da barace barace a kan tituna, tace in kaga mutane suna dambe a kan abinci kai kasan akwai babbar matsala a rayuwar mu baki daya, tace ya zama dole a hada karfi da karfi, don kawar da yunwa a tsakanin al’umma”
A madadin wadanda suka sami tallafin abincin, Hauwa’u Mohammed, tace sun godema Allah da ya kawu masu dauki ta hannun gidauniyar ‘Haidar’ cewa ba karamin walwala da annashuwa zai kawu masu ba a daiadai lokacin bikin na Sallahr layya.
Daga karshe, Aisha Abubakar da Rabiu Musa,
sunyi addu’ar Allah ya taimaki gidauniyar kan aiyukansu na alheri da jinkan talakawa.
Daga Adamu Shehu Bauchi