Bauchi: Dubban Magoya Bayan Dogara Sun Koma APC

Magoya Bayan Dogara fiye da Dubu sun Tsallaka Zuwa APC a Bogoro.

Kimanin mambobi fiye da dubu yayan Jamiyyar PDP ma goya bayan tsohon kakakin majalisar tarayya Barrista Yakubu Dogara, suka tsallaka zuwa Jam’iyyar APC a karamar hukumar Bogoro ta Jihar Bauchi.

Magoya bayan sun jadda da aniyarsu na bin Yakubu Dogara duk inda yasa kafa a hidimar siyasa, sun fadi hakan ne a wani babban taro na bikin sauyin shikar zuwa Jamiyyar APC a yankin mazabun na Bogoro.

Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar Bogoro Hakuna Rikaya yayin da yake karbar wadanda suka shigo jamiyyar tasu, yace “duk wanda yabi Dogara shine cikakken mai bin bayan demokradiyya ta gaskiya a yankinsu, yace shugabansu Yakubu Dogara ya watsar da jamiyyar PDP ne domin ci gaban yankinsa da kuma hikima irin na siyasa”.

Kana shugaban, ya ce duk wadanda suka shigo zasu yi aiki dasu kafada da kafada, domin samun hadinkai don Jam’iyyar APC ta lashe zabubukan kananan hukomomi dake tafe a cikin wan nan shekarar ta 2020.

Bulus Iliya, shine shugaban da ya jagoranci wadanda suka sauya shekar, a wajen taron, yace sune yan gani a kashen Dogara kuma siyasar uban gida ita suka sa a gaba.

“Muna jan hakalin gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulladir Mohammed, da Jamiyyar PDP da suyi gaskiya da adalci a wajen gudanar da zaben kananan hukumomi, domin shima anyi masa adalci a zaben 2019”.

Inda ya kara da cewa Bala ya lashe zaben gwanan jihar a karon farko, akan cewa duk wanda yaci zaben, to a bayyanashi ko da ba dan Jamiyyar PDP bane, acewar sa yin hakan shi ne zai kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin da ma dukkan kananan hukomomi ashirin na fadin Jihar.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply