Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya lashi takobin zakulu wadanda suke da hannu a cinhanci da rashawar da yayi katutu a biyan albashin ma aikata dana yan pansho, da kuma alawos-alawos a dukkannin fadin Jihar.
Yayi wan nan furucin ne a wani taro na mussaman da yakira a makon jiya, tare da masu ruwa da tsaki kan wan nan badakala na albashin da yaki ci yaki cinyewa a fadin Jihar.
Taron ya gudana ne a dakin taro na wajen saukan baki na rundunar sojin kasa dake Bauchi, (Command Guest House)
Bala Mohammed ya kara da cewa wan nan taro zai zama zakaran gwajin dafi domin kawo karshen wan nan barna da handama, da babakere, da wadansu suka jima suna satar kudin a tsarin albashin ma’aikatan Jihar.
“Ina kan cika alkawurran dana dauka, muna biyan albashi akan kari. adaidai 26 na kuwani wata, amma haryanzu hakarmu bata cimma ruwa ba, wan nan abun takaici ne cinhanci da rashawa karara a fili”, ya fada.
Bala yace “gwamnonin baya sunyi yunkurin kawo gyara amma shiru, ko dai basu da zimma, ko babu niyya na hakika, ko masu cin gajiyan hakan sun dabaibayesu”.
Gwamnan ya sanar da cewa “a shekarar 2015 albashin jihar ya kai biliyan 4.5 amma a yanzu albashin ya kai biliyan 7, kuma gashi ba a daukan aiki a jihar, duk da wasu sun yi murabus, wasu sun mutu, amma albashi yana hawa sama”.
Abun da mukayi a gwamnatance shine mun dauko masu hidimar kudi na musamman (DYNATECH IT Solutions) don gano masu hanu a ciki da kuma hukunta su bisa ga doka, Inji gwamnan.
Shugaban ma aikatan jihar Ahmed Abubakar Ma’aji, ya roki jamar jihar, musamman ma’aikata dasu ba gwamnati goyon baya don kawu karshen wan nan matsalar da take neman gagaraa kundila.
Suma anasu bayanin kampany da akaba ma alhakin gano badakalar da taki ci taki karewa a hidimar albashin jihar (DYNATECH IT Solution) a turance, sunce sun bankado ma aikata da yan pansho na buge inda akeyin sama da fadi da naira miliyan dari bakwai atashin farko, kana suka ce suna nan suna cigaba da aiki, kuma duk wanda bashi da hannu za abiyashi albashinsa ba tare da bata lokaci ba.