Bauchi: APC Ta Zargi Tafka Maguɗi A Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Jam’iyyar APC a karamar hukumar Darazo tayi zargin Jamiyyar PDP mai mulkin jihar da tabka magudi a zaben kananan hukumomi a jihar Bauchi

Adamu Maichi, shine Shugaban Jamiyyar APC na Darazo yayi zargin ne yayin zantawa da manema labarai a daidai lokacin da suke sa ido yadda zaben yake wakana a yankin.

“Zan iya gaya maku babu shakka jamiyyar PDP ta shirya tsaf don yin magudin da suka saba yi, a yanzu haka sun tare kayan zabe masu yawan gaske na gundumomi a karamar hukumar da runfunan kada kuri’u.

“Yanzun nan nake dawowa daga offishin yan’sanda na Darazo don kai koke na, abun mamaki, kawai sai naga wan nan dana ke cewa sun tare hanya da kayan zabe, sai gasu suna aikata hakan a gaban jami’an tsaro, ba su ce masu komai ba” Maichi ya fada.

Kana shugaban yace jamiyyar su APC baza ta amince da sakamakon zaben da bai cika shika-shikan inganci ba, muna Allah waidai da yin hakan.

Shiima anashi tsokacin tsohon kakakin majalisar jihar kuma dan majalisar dokokin jihar a yanzu, yace “akwai rashin tabbas da kuma tababa a sahihancin zaben nan, abun da shugaban Jamiyyar ke fada akwai kamshin gaskiya”

San nan yace, “banda rashin zuwan kayan aikin zabe a kan lokaci, da kuma irin kaiwa da komowa da su yayan jamiyyar suke yi tabbas biri yayi kama da mutum, hakan yasa shakku a dukkanin zukatanmu ta yadda suke so su gudanar da zaben”

A cewar wani jigo a Jamiyyar PDP Nasiru Darazo a yankin sunyi watsi da wan nan zargi a yankin karamar hukumar Darazon, inda yace “jamiyyarsu a matakin jiha tayi shiro tsaf don gudanar da zaben mai inganci da kowa zai amince da sakamakon, yace sun leko zasu sha kaye ne kawai suke korafi”

Kana ya kara da cewa “gwamna Bala yasha alwashin gudanar da zabe sahihi, yace ya tabbata duk wanda ya lashe zabe za a bayyana shi wanda yaci zaben ko da ba dan Jamiyyar PDP bane”.

Darazo yayi fatali da ikirarin APC kan zargin yin magudi a zaben na yau a halin yanzu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply