Bauchi: An Yi Nasarar Damƙe Wanda Ya Yi Wa ‘Yar Sa Fyaɗe

Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi sun damke wanda ake zargin ya aikata fyade ma yar’ cikinsa mai shekaru 15 da haihuwa, da kuma wadansu mutane su sha tara 19

Rundunar yan’sandan ta fitar da wan nan sanarwa ga manema labarai a ranar Talatan nan, ta hannun kakakin rundunar na Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil.

Kakakin Yan’sandan yace wani mai suna Umar Mohammed dan Shekara wanda ake kira (Wulas) wanda ke zama a Odoji Quarters a garin Azare an kamashi bayan ya yaudare yar’cikinsa mai tabin hankali da naira hamsin 50 kachal, ya tube mata kaya, yayi mata fyade, a cikin dakin dakin Mamanta, daga nan aka garzaya babban asibitin Azare da yarinyar, (an boye sunan ta) domin a duba lafiyarta. Kuma wanda ake zargin ya amince da laifinsa, Wakil ya fada.

Bugu da kari, ya bayyana cewa a ranar tara 9 ga watan nan na satumba ne aka samu rahoton a offishin yan’sanda na karamar hukumar Misau a cewar sa, Usman Adamu dan shekara 20 a yankin Nasarawa, sa’annan ya jaddada da hadin bakin Adamu Mohammed dana Nura Musa da kuma khalid Abdullahi. Kuma sunyi awon gaba da wata yarinya mai. shekaru 14 da haihuwa (an boye sunan ta)

Bayan sun karbi rahoto, wata tawaga, yace tuni suka iso inda wan nan abu ya faru, kana sunkaita babban asibitin Misau, wadanda ake zargin sun amsa aikata hakan, sanarwar ta kara da cewa sunyi nadaman aikata hakan, yace bincike na nan yana gudana, inda zasu inda za akaisu kotu da zarar an gama. Wakil ya fada.

Bugu da kari, Usman Musa mai zama a kauyen panshanu a Toro
da kuma rahoton yayi nuni da ranar 28 ga watan bakwai 7 cewa matarsa Hadiza wadda suke zaune a wuri daya, wacce take karbar maganin gargajiya a tashan badikko a karamar hukumar Toro.

Akan hanyanta ne aka tare ta akace sai ta kawo naira dubu goma N10,000
Inda tace bata dashi. Kakakin yan’sandan ya Shaida.

Daga nan ne mai suma Hussaini Adamu ya kamata da karfin tsiya yayi mata fyade, wanda ake, zargin shima a lokacin da ake tuhumarsa ya tabbatar da aikata hakan Mohammed wakil yace za a gurfanar dasu a kotu.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta