Bauchi: An Yi Nasarar Damƙe Wanda Ya Aikata Fyaɗe A Masallaci

Jami’an rundunar yan’sanda a jihar Bauchi sun sami nasarar damke wanda ake zargin yima yarinya yar shekara hudu fyade a cikin Masallaci, a ranar 03-09-2020 misalin karfe 11:30 na rana, a layin Aminu Street kusa da Titin Wunti a Bauchi.

Kakakin hukumar yan’sanda name jihar Bauchi Ahmed M. Wakil ya shaida ma manema labarai a yau bayan samum labarin aukuwar hakan daga bakin Jamilu Abdullahi dake zama a Igbo Quarters inda ya kai rahoton a ofishin yan’sanda na Township.

Sanarwar taci gaba da cewa, a wan nan ranar aka samu rahoton cewa mai suna Yusuf Bako dan shekara hamsin 50 wanda yake da zama a kan titin wanka a cikin garin Bauchi, ya yaudari yariyar sunanta (anboye) mai shekara hudu da haihuwa, ya shige da ita cikin Masallaci don yi mata fyade, kuma wanda ake zargin ya shiga hannun hukuma, kuma ya amince da laifin sa.

Yayin da jami’an tsaro ke tuhumarsa yace antaba kamashi, kuma ankaishi gidan kaso a shekarar 2001 da kuma shekarar 2015 akan irin wan nan laifin kuma yayi nadamar aikata hakan.

Hakanan ya shaida cewa, ya kasance a cikin wadanda gwamnatin jihar tayi masu ahuwa a gidan Yari, a farkon lokacin annobar corona.

Bugu da kari kwamishinan Yan’sandan Jihar Lawal Tanko Jimeta, ya kirayi al’ummar jihar dasu ci gaba da bama jam’ian tsaro goyon baya ta wajen lalubo labarai kan masu aikata masha’a tare da aikata laifufuka dabam dabam a cikin al’umma domi dakile su.

Har-ila yau, hukumar rundunar ta ba tabbacin samar da tsaro da kuma kare lafiyar jama’a da dukiyoyin su, tare da basu hadinkai domin inganta harkokin tsaro baki daya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply