Bauchi: An Yi Nasarar Ceto Matar Ɗan Majalisar Da Aka Kashe

Bayan kwanaki biyar da kisan gillar da aka yi wa dan majalisar mai wakiltar mazabar Dass a jihar Bauchi, Musa Mante Baraza da kuma garkuwa da aka yi da matarsa da dan sa mai shekara daya, an ceto su sannan sun sake haduwa da ‘yan uwansu a Baraza.

Labarin sakinsu an same shi ne daga bakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnan jihar Bauchi, Dr Kadan Salihu.

Ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce, “Alhamdulillah! An sako matan dan majalisar jihar Bauchi da aka kashe a kwanaki hudu da suka gabata.”

Ladan ya kara da cewa, “dan shi mai shekara dayan da aka sace tare da su duk an sako su. Gwamna Bala Mohammed ya bai wa likitoci da jami’an tsaro umarnin basu kulawa da tsaro.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin saboda su suka ceto wadanda aka sacen.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakili ya sanar da Tribune Online cewa, “tabbas jami’an ‘yan sanda sun ceto wadanda aka sace bayan bayanan sirri da suka samu daga masu kishin Dass.”

Ahmed Wakili ya kara da cewa, “mun samo su ne a wani kauye mai suna Bashi a cikin karamar hukumar da aka sacesu.

“Jami’an sun ceto su tare da mika su asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda ake kula da su.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce duk da ceto wadanda aka sacen da suka yi, har yanzu ba a samo wadanda ake zargi ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply