Mutane biyu ne Babbar Kotu Jihar Bauchi ta biyar 5 ta Yanke masu hukunci kisa ta hanyar rataya bisa aikata laifin kisa da kotun ta samesu da shi,a shakarar 2020, Kwamishinan shari’a na Jihar kima babban alkalin Jihar Alh.Yakubu Kirfi ya fadi hakan ne a wajen wani taron na masu ruwa da tsaki a harkokin shari’a da ya wakana a Jihar.
Kana yayi bayanin cewa
daya daga cikin wadanda aka zartar masu da hukunci Kisan Mai suna Umaru Jauro, kan aikata laifin Kisan kai da gangan ne da wata manufa na amfani da gawar
Ya kuma kara da cewa shima dayan Mai suna Juraidu an same shi da laifin kashe Yar cikinsa domin amfani da ita
Yakubu Kirfi ya nuna cewa akwai wani mai suna Shamsudeen Umar da Kotunhar ila yau ta same shi da laifin aikata fyade ma wata yarinya, Wanda shima kotun tuni ta Yanke masa hikunci zaman gidan yari har tsawon rayuwarsa
Haka nan Kirfi ya kara da cewa babban kotun Jihar ta kama wasu da laifin Sulaiman Dawa da Abdullahi Sani da aikata fashi da makami da kima yima wata yarinya fyade dukkanimsu an yanke masu shekaru bakwai 7 da goma 10 a gidan kaso.
Kwamishinan shari’ar ya jaddada aniyar Gwamnan Jihar Bala Mohammed a
Shekarar 2020 yayi ma wasu fursunoni ahuwa su kimanin 106 tare da biua masu kudin tara da akayi masu a karkashin kwamitin bada shawarwari kan rage chunkoso a gidajen yari a fadin Jihar.
Ya karkare da cewa maaikatar shari’ar ta Jihar ta samu korafe korafe kimanin 164 a shekarar bara ta 2020
Yace ansamu kararraki 35 a kotun daukaka kara, guda talatin 30 kuwa a kotun shari’a ta ma’aikata, talatin da hudu 34 kuwa an rabasu ne a babban kotun Jihar, yace sauran kuwa ana kokarin karasa shari’o’insu a shekarar da ake ciki.
Daga Adamu Shehu Bauchi