Gwamnatin Jihar Bauchi ta Soke Kwangilar gina Fadar Katagum dake garin Zaki nan take, ba tare da wani dogon bincike ba,
Gwamnan Jihar ne Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana hakan a Kofar fadar Hakimin katagum, yayin da yake ran-gadin duba ayyukan more rayuwa a yankin.
Gwamnan Bala wanda yace Kwangilar zata lakume naira miliyan 75 ne, san nan ya nuna rashin jin dadin sa game da ayyukan da ya gani ma idanunsa a yayin ziyarar, yace ko kadan dan Kwangilan bai kyauta mashi ba.
Kana Yace “Sauran fadojin da muka bayar izuwa yanzu duk an kammala su, me yasa wan nan baza a gamashi cikin lokaci ba, saboda haka na soke wan nan Kwangilar, kuma zamu kawo wan dai zaiyi daga cikinku, zaku ga yadda zamu gauraya dashi”.
Har ila yau, yace “alakarmu da mutum na
siyasa dabam, na sanayya dabam, na aiki kuma shima dabam, amma bazan yadda ina kallo ba, anayin abinda bai dace ba”
Anashi jawabin Hakimin katagum Usman Mahmud yace tunda Gwamna ya zarta da hukunci, shi babu abin da zaice saidai godiya ma Allah da kuma yaba ma gwamnan kan ayyukansa na more rayuwa,
Hakimim yayi addu’a tare da fatan alheri ma gwamnan, cewa Allah ya bashi ikon kammala ayyukan da ya faro ma al’ummar Jihar Bauchi, domin samun ci gaba mai dorewan.
Suma Al’ummar yankin da sukayi dafifi a Kofar fadan, sun jinjina ma gwamna Bala kan Jajircewarsa ta wajen ayyukan raya al’umma baki daya.
Daga Adamu Shehu Bauchi