Rahotanni sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda ta kama makisan ɗan majalisar dokokin jihar Bauchi, Musa Baraza.
An kuma tattaro cewa an kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da Yaya Adamu, yayan gwamnan jihar.
An saki Adamu wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 25 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamna Bala Mohammed ne ya sanar da kamun masu laifin a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, lokacin da babban faston katolika na jihar Bauchi, Most Rev.
Bishop Hilary Dachelem ya ziyarce shi a gidan gwamnatin Bauchi, babbar birnin jihar.
Wasu yan bindiga ne suka harbe Baraza wanda ke wakiltan mazabar Dass har lahira, a gidansa da ke Baraza a ranar 14 ga watan Agustan 2020.
‘Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da matansa biyu da yarsa mai shekara daya amma sai suka sake su daga bisani.