Bauchi: An Gurfanar Da Matasa 30 Bisa Zargin Aikata Manyan Laifuka

Kwamishinan Yan’sanda na Jihar Bauchi Sylvester Alabi ya Gurfanar da matasa su kimanin Talatin 30 Bisa ga Zargin aikata manyan Laifuffuka da suka hada da garkuwa da mutane, satar shanu, fashi da makami, kwacen wayar tafi da gidanka. da sauransu.

Kwamishina Alabi, ya ja hankalin al’umma da su cingaba da bama Jami’an tsaro goyon baya wajen bankado masu aikata laifi, don samun inganci a rayuwar Al’umman gari baki daya,

A lokacin da yake ma Yan’jarida Karin haske kan wadanda ake Zargin yace dukkanin su, ankamasu ne kan aikata fashi da amakami da kwacen wayar hannu, tare da cin zarafin jama’ar unguwani da dama, ba dare ba rana, yace Kuma abin takaicin shine duk masu aikata laifin matasa ne yan kasa da shekaru ashirin da haihuwa ne suka fi yawa.

A cewar Alabi dukkanin wadanda aka Gurfanar, rundunar Yan’sanda za taci gaba da bincike, inda daga karshe zasu mika su hannun kuliya manta sabo don yi masu shari’a dai-dai da laifin da suka aikata, domin yanke masu hukunci,

Su kuwa wadanda ake Zargin, lokacin da manema labarai ke tuhumarsu a shalkwatar Yan’sandan, wadansun su sun musanta Zargin da ake masu, da cewa dukan tsiya ne yasa su suka amsa Zargin, amma ko kadan ba haka abin yake ba, inda wasu Kuma sukayi nadamar aikata laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Kwamishinan Yan’sanda, ya karkare da cewa Jami’an tsaro na aiki a koda yaushe don zakulu bata gari, tare da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, a dukkan fadin Jihar Bauchi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply