Bauchi: An Damke Malamin Da Ya Soki Izala Kan Harka Da ‘Yan Siyasa

Labarin dake shigo mana daga jihar Bauchi na bayyana cewar Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun kama gami da tsare wani malamin addinin musulunci mazaunin garin Bauchi mai suna Abubakar Baba Karami bisa zarginsa da wasu kalamai kan ‘kungiyar izala inda ya nuna malamanta suna mu’amala da ‘yan siyasa.

Malamin wanda aka fi sani da Afakhallah yayi wannan maganar ne akan mumbarin masallacin Juma’a a wani masallaci a jihar Bauchi a ranar 18 ga watan Nuwanban 2022.

Ya bayyanna sunan Kabir Muhammad Gombe da Abdullahi Bala Lau da Ahmed Sulaiman a matsayin masu ci da addini da kuma kar’bar ku’da’de a wajen ‘dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar Afakhallah yace malaman sunyi watsi da halayyarsu ta malanta tare da neman abin duniya da kuma biyewa ‘kyale’kyalenta.

Lokacin da yake maida martani kan zargin da afakalla yayi masa, ya musanta zargin tare da tabbatarwa da afakallah cewa suna neman kudi kuma suna da kudi. Sheik Gombe ya zargi Afakhallan da rashin sani tare da kuma tabbatar masa da cewa zai maka shi a kotu dan ya tabbatar da zargin da yayi musu.

“Muna zaman kanmu ba’a kasan kowa muke ba, kuma kaje Gombe ka tambaya; ina biyan sama da ma’aikata 200 a kasa na”.

Lauyoyin masu kara sun tabbatar da cewa anyi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen batawa wa’dancan mutane suna tare da cin zarafin su. “A cikin wa’azinsa ya kira malaman ‘kungiyar izala da sunaye ir-iri wanda basu da da’din ji”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply