Bauchi: An Damƙe Tsofaffin Da Suka Yi Wa Ƙaramar Yarinya Fyaɗe

Rundunar Yan’sandan jihar Bauchi ta samu nasarar chapke wadanda ake zargin sun yi lalata da karfi ma wata yar shekara 13 a kusa da Otel din Sindaba dake garin Bauchi.

Kakakin rundunar yan’sandan Jihar Bauchin Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar ma manema labarai aukuwar wan nan al’amari.

Cikin sanarwar kakakin yache sun sami rahoton take bakin wani bawan Allah mai suna Rabi’u Musa, wanda ke zaune a Sabon Kaura, ya basu labarin yadda mutanen Ibrahim Musa dan shekara 63 da Nuhu Isah mai Shekaru 56 suka yaudari yarinyar yar shekara 13 da kudi naira dubu daya da dari uku (N1300) suka shigar da ita wani gida da ba agama ginawa ba daura da Otel din Sindaba a rukunin gidajen gwamnati (new GRA).

Rahoton ya ce Ibrahim Musa wanda ake zargi na farko yana gadi ne a wan nan gidan da ba a gama ba, inda suka aikata fyaden, a matsayin (security gate man)

Ahmed Wakil ya ci gaba da cewa bada bata lokaci ba jami’an yan’sandan suka nufi wan nan wuri suka yi sa’an chapke wadanda ake zargin, kuma sun amsa laifinsu bayan an tuhume su, kana suka garzaya asibiti da wacce akayi ma fyaden don duba lafiyarta .

Wakil ya ce Kwamishinan yan’sanda na jihar Lawal Tanko Jimeta yasha alwashi mika su zuwa kotu domin yi masu hukuncin da doka ta tanada don masu cin zarafin mata a jihar Bauchi.

Bugu da kari, haka nan Lawal Tanko Jimeta ya tabbatar da kama mutum bakwai 7 da ake zargin su da aikata manyan laifuffuka duka a cikin sati biyu da suka wuce a fadar jihar.

A cewarsa da zarar rundunar ta kammala bincike za akaisu kutunan shari’a domin yanke masu hukunci, kana Jimeta ya yaba da kokarin jamar gari da kuma kara masu karfin gwiwa da sun gani to suyi magana da wuri don jami’ai tsaro su dauki matakin da ya dace.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta