Rundunar ‘Yan’sanda na Jihar Bauchi sun sanar da kama wani matashi dan Shekarar 28 da haihuwa mai suna Rufa’i Yunusa dake kauyen Rumbu a karamar hukumar Ningi da zargin kashe yara guda hudu masu kananan Shekaru 2 zuwa 4 don yin tsafi dasu.
Rundunar Yan’sandan ta ce sun kamashi ne biyo bayan sumame a ranar Laraba da ta wuce, wanda jami’an sukayi a kauyen bayan mutanen garin sunyi karar shi a chaji ofis na garin.
Kakakin rundunar Yan’sanda na Jihar Bauchin SP. Mohammed Wakil, ya tabbatar ma da manema labarai aukuwar wan nan al’amari.
Kana ya kara da cewa a ranar Talata 16 ga watan nan da muke wani Isyaku Ahmed ya kawu labarin cewa ya kai Yar’sa Maimuna wacce take fama da rashin lafiya, sai shi Rufa’i yace yarsa tana fama da ciwon shafan al’janu don ayi mata magani, kuma yasha alwashin zai warkar da ita.
Daga nan sai shi Rufa’in ya bukaci Malam Isyaku Baban Maimuna ya bashi naira dubu goma N10,000 a matsayin kudin magani, daga baya sai kawai ya dawo Yana cewa Maimuna ta bace a lokacin da yake yi mata magani ya meme ta bai ganta ba.
Ahmed Wakil, yace bayan samun labarin, jami’an Yan’sandan suka nufi jejin suka yi bincike suka gano jikin yarinyar (Maimuna) anyi gunduwa-gunduwa da ita, inda suka yi asibiti da ita inda likita ya tabbatar da mutuwarta.
Kakakin ya kara nuni da cewa, tuni sun kama shi da aikata laifin, a yayin binciken shi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin
Kakakin yace bayan sun fadada bincike, wanda ake zargin ya shaida cewa ba ita ce kadai ba akwai yaran da ya yaudari iyayen su, suka auka cikin wan nan aiki ta’asa.
Ya ce a cikin kayan da aka kama shi dasu akwai wuka da kayan yara ashirin da shida 26 a cewarsa, rundunar tana ci gaba da bincike, zasu kaishi kotu domin tuhumarsa da kuma yanke mashi hukunci kan laifin da ya aikata
Daga karshe rundunar ta ja kunnen al’umma da su rika sanya ido sosai akan yaransu da kuma la’akari da duk wanda yace shi malamin ne mai bada magani ko wani iri ne.
Daga Adamu Shehu Bauchi