Bauchi: An Dam?e Matasa Masu Addabar Jama’a

A ranar ashirin da bakwai 27 ga watan janairun nan ne, Jami’an tsaro na Yan’sanda masu bin kwakwaf wadan ake kira Rapid Response Squard (RRS) a turance suka Kai sumame ma wasu gungun matasa da suka Addabi mutane unguwan Abujan Kwata, Kofar Wambai da kuma wasu sassan Jihar da kwacen wayoyi da hallaka su.

Kakakin rundunar Yan’sanda na Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, a madadin kwamishinan Yan’Sanda Lawan Tanko Jimeta ya fitar da sanarwar ga manema labarai, inda yace a dalilin sumamen sun sami nasarar chapke akalla matasa ashirin da uku 23 a maboyar su, a cikin fadar Jihar,

Inda yace sun addabi al’umma tare da fitinan Jama’a da dama a unguwani, wadan nan matasa basu da wani aikin yi illa su tare mutane, mace ko magidanta a cikin lungu su kwace masu kudi, ko waya, ko jaka ta mata da dai sauransu.

Wakil ya kuma ce matasan sukan yanki mutum su barshi cikin jini ko wani halin da mutum bazai iya tashi ba, Wanda hakan ka iya kashe mutum har lahira nan take.

Bugu da kari, ya kuma shaida cewa, a ranar sha bakwai ga watan dayan nan, Yan’sanda da suke zagayawa soko da lunguna sun kama barayin Kekenapep da Mashina tare da muggan makamai a kimba (Junction) wanda sun kasa fadin dalilin rike wadan nan makamai.

Kakin rundunar daga karshe yace, dukkan wadan nan da aka Kama suna aikata irin wadan man laifuffuka, zasu dandana kudarsu.

Kana yace tuni hukumar Yan’sandan ta aika su zuwa bangaren binciki da akafi sani da suna State Criminal Investigation Department (SCID) a turance, domin kammala bincike da samun bayanai, wanda daga bisani za ta mika su zuwa kotu don yanke masu hukunci.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment