An Fara Rushe Babban Masallacin Juma’a Na Shekh Dahiru Usman Bauchi Da Gidajen Makwabtansa Domin Gina Masa Sabon Masallacin Juma’a Da Makarantar Zamani A Jihar Bauchi
A yau Lahadi 4/7/2020 ne aka tashi da aikin rushe babban masallacin Juma’a na Shekh Dahiru Usman Bauchi da gidajen makwabtan sa a jihar Bauchi wanda aka saya domin aikin fadada Masallacin sa da kuma gina babbar makaranta ta zamani.
Aikin da wani Bawan Allah mai yawan alheri ga al’umman a jihar Bauchi ya dauki nauyi wanda zai Lashe milyoyin nairori, za a gina masallacin Juma’a na zamani mai girman gaske da tsari.
Ubangiji Allah ya sa a kammala lafiya. Shi kuma wannan Bawan Allah dake aikin alheri masu girma ga a’lumar jihar Bauchi, Allah ya saka masa da alheri, ya sa ya kammala aikin sa na Gwamnatin tarayya lafiya. Ya dawo ya cigaba da bada gudummawa ma jihar sa.