Bauchi: Ɗahiru Bauchi Ya Jagoranci Zikirin Sabuwar Shekarar Musulunci

An gudanar da taron Zikiri na shekarar (1442) a jihar Bauchi wanda ya kasance a gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake titin zuwa Gombe. Inda mabiya darikar Tijjaniya suke zuwa daga sassan kasar nan.

Taron wanda ake yi duk shekara a garin Bauchi, bana ma an gudanar da irin sa a gidan Shehu Dahiru, don murna da zagayowan sabuwar shekarar Musulunci da kuma yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Allah ya amfanar da mu, ya karbi addu’o’in da aka yi a wurin, ya ba mu zaman lafiya a kasar mu baki daya. Amiin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply